Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Morocco, Moroccan Football Federation, ta bayyana cewa yanzu ta karkata hankali wajen shirya karɓar bakuncin gasar Women’s Africa Cup of Nations ta 2026.
Hakan na zuwa ne bayan kwamitin ɗaukaka ƙara na hukumar kwallon kafa ta Afrika ya soke nasarar da Senegal ta samu a wasan ƙarshe na gasar kofin Afrika, tare da bai wa Morocco kambun gasar.
Hukuncin ya biyo bayan ficewar Senegal daga wasa saboda zargin hukuncin fanareti, abin da dokokin gasar suka ɗauka a matsayin mika wuya.
Hukumar ta Morocco ta ce ba ta ƙalubalanci sakamakon wasa ba ne, sai dai ta nemi a mutunta dokoki da adalci.
A halin yanzu, Morocco ta ce tana da kwarin gwiwa wajen karɓar bakuncin WAFCON 2026, wacce aka dage daga watan Maris zuwa 25 ga Yuli domin inganta shirye-shiryen gasar.
Najeriya ce ke riƙe da kambun gasar bayan Super Falcons sun doke Morocco a wasan ƙarshe, inda suka lashe kofin karo na 10.
