Wasu daga cikin al’ummar karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a Arewa Maso Yammacin Najeriya na rokon Gwamnatin kasar da ta fitar da su daga cikin kasarta ta mayar da su kasar Nijar.
Al’umma na wannan kiran ne dangane da hali na rashin tausayi da suke tunanin gwamnatin kasar na nuna masu kasancewarsu suna kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Wani mutum mai suna Abdulaziz Muhammed mai saida nama ya ce, gwamnati bata dauke su bakin komai ba, bata damuwa da matsalolinsu sai dai in lokacin siyasa ya zo a ke jawo su jiki ana nuna masu su yan Najeriya ne.
Ya ce amma da zaran lokacin siyasa ya wuce to shikenan sai a mayar da su kamar yan kasar ta Nijar.
Ya ce hatta masara ko garin-rogo ba a bari suna zo masu a Jibia.
“Mu abinda muke so kawai a fitar da mu daga Najeriya a mayar da mu cikin Nijar, tunda dai mu ba kaunar mu, mi yasa lokacin siyasa ake neman kuri’armu amma da zarar an gama zabe kuma sai a koma yi mana cin kashi.” in ji shi.
Mutanen Jibia dai na zargin yadda jami’an tsaro ke hana abinci yana zuwa gare su daga bakin kofar Guga da ke cikin birnin Katsina.
Sun ce yunwa da talauci na kara addabar yankinsu da jama’arsu baki daya.
