Daya daga cikin wadanda suka jima suna yi wa Masallacin Manzon Allah S.A.W hidima Agha Habeeb Muhammad al-Afari, ya rasu a Larabar nan.
BBC ta ce, Shafin Tiwita na HaramainSharafain ya ruwaito cewa Agha Habeeb shi ne ke kula da dakin da kabarin Mazon Allah S.A.W yake.
Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa a masallacin Annabi (S.A.W) da ke Madina.
