Jam’iyyar NNPP da ƙungiyar Kwankwasiyya sun zargi wasu ’yan daba da ake alaƙanta su da jam’iyyar APC da kai hari kan mambobinsu yayin wani taron siyasa a ƙaramar hukumar Rogo da ke Jihar Kano.
A cikin sanarwa da suka fitar a ranar Lahadi, sun ce harin ya faru ne a gundumar Ruwan Bago lokacin da mambobin NNPP ke karɓar wani fitaccen ɗan siyasa da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP.
Jam’iyyar NNPP ta ce harin ya jikkata mambobi 11, yayin da aka lalata motoci biyu tare da sace wayoyin hannu da dama.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Ibrahim Karaye, ya yi Allah-wadai da lamarin tare da buƙatar hukumomin tsaro su binciki abin da ya faru tare da hukunta masu hannu a ciki.
Shi ma mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Sale Mohammed, ya ce wasu ’yan daba dauke da makamai ne suka tarwatsa taron lumana da aka shirya domin karɓar masu sauya sheka zuwa NNPP, inda aka jikkata mutane da dama tare da lalata motoci da wasu kadarori.
Ƙungiyoyin biyu sun bukaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yayin da har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a samu martanin jam’iyyar APC a Kano ba.
