PDP Ta Zargi APC Da Samar Da Rumfunan Zaɓe Na Bogi A Imo

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Imo, Ray Emeagha, ya yi zargin cewa akwai rumfunan zabe na jabu a jihar.

Emeagha ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Sunrise Daily, inda ya kara da cewa jam’iyyar ta sanar da INEC kan batun a 2019.

Ya ce, “A shekarar 2019 mun gano cewa akwai rumfunan zabe na jabu a jihar Imo. Mun sanar da INEC, ni kuma na yaba musu saboda sun shigo sun gyara (ta), amma yau (wato APC) sun koma irin wannan tsarin.

“Na biyu, shin ba gaskiya ba ne cewa ana tafka magudi a bayanan INEC? Karamar hukumar da ta yi fama da rashin tsaro inda kusan kowace al’umma ke cikin bala’i kuma ta yi rajista kasa da 12,000 a shekarar 2019 kuma a yanzu ta ce ta yi rajistar 86,000.

“Ƙaramar Hukumar Oru ta Gabas ce, musamman unguwar Gwamnan Jihar da ta yi rajistar masu jefa ƙuri’a 46,000 amma tana da 6,000 kacal shekaru uku da suka wuce. Yana kan gidan yanar gizon INEC?”

Emeagha ya kuma yi wa ma’aikatar yada labaran jihar ba’a da kiranta da cewa wata masana’anta ce a gidan gwamnatin Imo wadda aikinta shi ne kera karya da farfaganda.

Da yake mayar da martani kan zargin, kwamishinan INEC na kasa, Mista Festus Okoye, ya ce akwai rumfunan zabe 176,846 a fadin kasar inda za a tura ma’aikata da kayan aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *