Peter Obi Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Kan Kalaman Da Abokin Takarar Sa Ya Yi Kan EndSARS

Peter Obi Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Kan Kalaman Da Abokin Takarar Sa Ya Yi Kan EndSARS

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya mayar da martani akan jawabin da mataimakin takararsa yayi Datti Baba-Ahmed akan Harbin da akayi Lekki Toll gate lokacin zanga-zangar EndSARS.

Idan dai za’a tuna, Baba-Ahmed a yayin da ake tattaunawa dashi gidan talabijin na Channel TV a cikin shirin Siyasar mu a yau a makon da ya gabata, ya ce amfani da kalmar ‘kisan kiyashi’ akan harbe-harbin daya wakana a lokacin zanga-zangar EndSARS a watan Oktoba na shekarar 2020, abune da bai faru ba.

Wannan Kalami ya haifar munanan maganganu daga wasu ƴan Najeriya musamman Matasa, wadanda suka yi imanin cewa bayanin sa ƙaryata kisan da aka yi ne a Lekki Toll gate.

Amma a lokacin da Obi yake amsa tambayoyi a gidan talabijin na Arise Tv a cikin shirin barka da safiya, yace yanzu ne yake jin wannan bayani na Datti akan kisan daya faru.

Yace anyi abubuwa da dama akan kuskure a baya, wanda suna buƙatar a nemi yafiya akan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *