A wani abin da ake ganin ci gaba da gwabzawa fada tsakanin su, mayakan kungiyar IS a karshen mako sun kai hari a yankunan ‘yan Boko Haram, inda aka ce sun kashe shida daga cikinsu.
A wani samame da ISWAP ta kai a sansanin ‘yan Boko Haram da ke Gajibo, wani gari mai tazarar kilomita 95 daga arewa maso gabashin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun kashe wasu 6 da suka ayyana a matsayin “kafirai”.
A cewar Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, maharan sun kuma kwato bindigogin AK47 guda biyar daga hannun ‘yan ta’addan na Boko Haram.
ISWAP dai ta sha kai hare-hare da dama a kan ‘yan ta’addar Boko Haram a cikin rigingimun da suke ci gaba da yi, wanda ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.
Tabarbarewar fadace-fadacen da ake yi tsakanin kungiyoyin masu ikirarin jihadi, na iya kai su ga halakar da ba za a iya jurewa ba, kamar yadda kungiyar ISWAP mai tayar da kayar baya ta sha alwashin fafatawa da mambobin tsohuwar kungiyarta fiye da ma sojojin Najeriya.
