Sarki Charles: An tabbatar min shinkafa dafa duka ta Najeriya ita ce mafi daɗi

Sarkin Birtaniya, King Charles III, ya bayyana cewa an tabbatar masa da cewa shinkafar jollof ɗin Najeriya ce mafi daɗi a nahiyar Afirka kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen liyafar ƙasa da aka shirya domin girmama Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da mai ɗakinsa, Oluremi Tinubu, a ƙasar Birtaniya.

A halin yanzu, Tinubu na wata muhimmiyar ziyarar ƙasa ta kwanaki biyu a Birtaniya.

Jollof wani shahararren abinci ne na yankin yammacin Afirka da ake dafawa da shinkafa, tumatir, albasa da barkono, tare da kayan kamshi irin su thyme da curry. Ana yawan gabatar da shi a bukukuwa da taruka tare da nama, ko salad.

Sarkin ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna Birtaniya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban ƙasar.

Ya ce, “Mu a Birtaniya muna alfahari da dimbin ‘yan asalin Najeriya da suka zaɓi zama a nan, kuma yanzu suna taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban kamar kasuwanci, fasaha, ilimi, doka, kimiyya, wasanni, adabi da fasaha.”

Sarkin ya ƙara da cewa ya haɗu da ‘yan Najeriya da dama da ke bayar da gagarumar gudunmawa a muhimman cibiyoyi na ƙasar.

Haka kuma, ya bayyana cewa a kwanan nan ya karɓi bakuncin wasu ‘yan Najeriya a fadar St James’s Palace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *