Shugaba Buhari Ya Nada Mutane 4 A Matsayin Daraktocin CBN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane hudu a matsayin wadanda ba na zartarwa ba a matsayin daraktocin babban bankin Najeriya CBN.

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Yuli kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren taron ranar Talata.

Buhari a cikin wasikar, ya ce an gabatar da bukatar ne bisa ga sashe na 10 (3) (a) na dokar babban bankin Najeriya (Establishment) na shekarar 2007.

Wadanda aka nada sun hada da: Farfesa Mike Obadan (Kudu maso Kudu), Farfesa Justitia Nnabuko (Kudu maso Gabas), Farfesa Ummu Jalingo (Arewa-maso-Gabas) da Mista Adeola Adetunji (Kudu maso Yamma).

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *