Yan bindiga Sun Halaka Mutu 3 Tare Da Daukar Wasu Yan Sa Kai Da Yara 5 A Taraba

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Mazauna Babban birnin Taraba wato Jalingo sun fuskanci tashin hankali, yayin da Yan bindiga suka Kai Hari a garin suna harbin kan mai uwa da wabi da tsakiyar daren ranar Litinin din nan.

Majiyar Jakadiya, ta fahimci cewa Yan bindigar sun Kashe Mutum 3 tare da dauke yara Mata 5 da kuma wasu shuwagabanni Yan kungiyar Sakai a garin.

Wannan lamari ya faru a ranar Daren Asabar da Litinin a wurare daban- daban Jahar.

Jaridar Daily Trust, ta bada rahoton cewa da tsakiyar Daren ankashe wani mutum tare da jami’in Dan sanda a Lasandi, BabaYau da kuma Sabon Gari.

Yan bindiga sun Dauke wani shugaban kungiyar Yan Sakai Mai suna Bashir tare da wasu yara Mata biyar da misalin Karfe 1:30am a titin mahadar samina a Daren ranar litinin.

Rohoton ya bayyana cewa, Yan bindiga akan mashina sun shiga yankin tare da harbi a sassa daban daban kafin zuwa mazaunin shugaban kungiyar Sakai din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *