Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga ‘yan jam’iyya a taron yankin kudu maso kudu na jam’iyyar APC da aka gudanar a Asaba, a jihar Delta.
Shugaban majalisar dattawan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da wannan shiri.
Akpabio ya kuma ce birnin Warri ne zai zama babban birnin sabuwar jihar Delta idan aka ƙirƙiri jihar Anioma.
