Sojoji Sun Damƙe Ƴan Bindigar Ƙasashen Waje A Katsina
Hedikwatar tsaro a ranar Alhamis ta ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kama wasu ƴan ƙasashen waje guda biyar da ake zargin ƴan bindiga ne a yayin wani sintiri na yau da kullum da aka kai a ƙaramar hukumar Jibia ta Katsina.
Wadanda ake zargin dai sun hada da Muritala Wada da Saminu Sani da Shamisu Adamu da Salisu Saadu da kuma Usman Ibrahim.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake yiwa Manema Labarai ƙarin haske kan ayyukan sojojin da ke fadin kasar tsakanin 28 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta.
Ya kuma ce an kama mai bada bayanan sirri ga Ƴan Bindiga da Sashen Jami’an tsaron farin kaya ke nema ruwa Jallo.
Onyeuko ya ce, “Dakarun Operation HADARIN DAJI da ke shiyyar Arewa maso Yamma na kasar nan na ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar kai samame na yaki da ƴan ta’adda domin fatattakar ƴan bindiga da ƴan ta’adda.
“A ranar 25 ga Yuli, 2022, sojoji da ke sintiri na yau da kullum sun kama wasu mutane biyar da ake zargin ƴan bindiga ne daga kasashen waje da suka haɗa da Muritala Wada, Saminu Sani, Shamisu Adamu, Salisu Saadu da Usman Ibrahim a Jibia a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
“Bugu da kari, a tsakanin 31 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta, 2022, sojoji sun kama wani Malam Yahaya, wani fitaccen mai baiwa ƴan bindiga da ke cikin jerin sunayen jami’an tsaron farin kaya da ke aiki da ƴan bindigar kan hare-haren da aka kai a yankin Sabon Brini na jihar Sakkwato. . Sojoji sun kwato shanu 161, rakuma 8, da manyan kaya daga hannun ‘yan ta’adda bayan wata arangama da suka yi a Zango a karamar hukumar Shinkafi.”
Ya ce ‘yan ta’addan Boko Haram 1,755 da iyalansu da suka hada da maza 280, mata 523 da yara 952 ne suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a cikin makon da ya gabata, inda ya ce duk ‘yan ta’addan da suka mika wuya da iyalansu an bayyana su tare da mika su ga sojoji.
Onyeuko, ya ce sojojin Najeriya na Operation Delta Safe sun kama wasu manyan ‘yan fashin teku biyu da aka fi sani da Fagha Golden da ake kira fine boy a kauyen Nonwa da ke karamar hukumar Tai da kuma Victor Elkanah wanda aka fi sani da Victor Padi a asibitin Pharzy Spring Diagnostic and Wellness Hospital, One- Karamar Hukumar Eleme ta Jihar Ribas.
