Sojoji Sun Damƙe Sinƙi-Sinƙi na Tabar Wiwi 98 Jihar Yobe
Dakarun bataliya ta 159 Task Force Battalion da ke Geidam a jihar Yobe sun tare wata mota dauke da fakiti 98 na Tabar Wiwi da darajar ta takai na miliyoyin Naira.
Birgediya-Janar Umar Muaza, shugaban ma’aikata na sashin Hadin Kai da ke Damaturu ne ya bayyana hakan ga Manema Labarai a ranar Litinin a yayin mika kayayyakin baje kolin ga jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar.
Ya ce masinjan da ke jigilar haramtattun kwayoyi ya yi watsi da motarsa, ya yi ta kai-komo yana ganin dakarun da ke sintiri.
Da yake karbar fakitin guda 98 da aka kama a madadin hukumar NDLEA reshen jihar Yobe, Ogar Peter ya ce farashin titin kowane fakiti ya haura Naira dubu N50,000.
“Mun yi matukar farin ciki da cewa, an fitar da wannan adadin daga wurare dabam dabam. Idan da ta je Inda za’a kaita, da an yi amfani da ita wajen rura wutar kalubalen tsaro,” inji shi.
Peter ya kara da cewa kamun da sojojin suka yi na miyagun kwayoyi ya nuna irin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
“Rundunar sojin Najeriya na bayar da goyon baya sosai a fafutuka da kuma yaki da matsalar safarar miyagun kwayoyi.
