Tasirin Gwamna Fintiri Na Ƙara Zama Muhimmi Wajen Zaɓen Wanda Zai Zama Sabon Gwamnan Jihar Adamawa 2027

Wani sabon rikici na siyasa na ƙara bayyana cikin jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, sakamakon fara fafatawa kan buƙatar neman kujerar gwamnan Jihar tun yanzu.

Rikicin ya ƙunshi ɓangarori biyu masu ƙarfi wanda ya haɗa da magoya bayan NSA, Nuhu Ribaɗu da kuma na gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya sauya sheka zuwa APC tare da ɗumbin magoya bayansa, kamar yadda Arewa Media ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ribaɗu na son a ba su damar tsayar da ɗan takara, yayin da bangaren Fintiri ke ganin rinjayensu a cikin jam’iyyar ya ba su wannan dama. Wannan yanayi na ƙara haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar a Jihar.

Masu lura da al’amura sun bayyana cewa Jihar Adamawa na da muhimmanci ga APC a matakin ƙasa, musamman ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Sai dai sun jaddada cewa nasara a jihar ba za ta samu ba sai an samu ɗan takara da jama’a za su amince da shi.

Fintiri na ci gaba da bayyana a matsayin jigo a siyasar Jihar, duba da nasarorin da ya samu a zaɓukan 2019 da 2023, duk da ƙalubale mai yawa. Shigowarsa APC ya sauya tsarin ƙarfin iko a jam’iyyar, inda ya zo da gagarumin goyon baya da ya rinjayi membobinta na asali.

Har ila yau, an bayyana cewa ƙwarewarsa wajen tafiyar da harkokin tsaro da magance matsaloli kamar Boko Haram, sace-sacen mutane da rikicin manoma da makiyaya, na daga cikin abubuwan da suka ƙara masa karɓuwa a wajen jama’a.

A ƙarshe, masana siyasa na ganin cewa tasirin Fintiri zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai zama gwamnan Adamawa na gaba, domin duk wanda ya samu goyon bayansa na da babbar damar samun nasara a zaɓe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *