Ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya ta ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya mayar da jakadun ƙasar da ke ƙasashen ƙetare gida.
Bayanin hakan na zuwa ne a cikin wata sanaraw da fadar shugaban kasar ta wallafa shafinta na Twitter da a yanzu aka zanja ma suna zuwa X, ta ce umarnin ya shafi dukkan jakadun ƙasar a ƙashen ƙetare, in ban da wakilan ƙasar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a New York da Geneva, sakamakon babban taron Majalisar da za a yi nan gaba cikin wannan wata.
