Kimanin jami’an tsaro 34 ciki da jami’in soja guda sai mambobin kungiyar ‘yan sintiri 33 ne suka rasa rayukansu a’ yan watannin da suka wuce a yayin arangama da ‘yan ta’adda a bangarori daban-daban na jihar.
A yayin da yake jawabi a wajen taron bayar da tallafi ga iyalan wadanda suka rasu wajen yaki da’ yan ta’addan, Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya koka dangane da yadda aikace-aikacen ‘yan ta’adda ke ci gaba da kasancewa musamman ma a kauyukan da ke kusa da dazukan jihar.
Dikko Raɗɗa ya ce, matsalolin da ta’addanci ya jawo a jihar shi ne ya saka gwamnatinsa sanya bilyoyin naira don ganin an wasu kayayyakin yakar’ yan ta’addan da sauran wasu abubuwan da zasu taimaka wajen shawo kan matsalar.
Raɗɗa wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, ya ce gwamnatinsa zata yi iya yinta don ganin ta kawo karshen rashin tsaro a fadin jihar.
Ya kara da cewa, Wannan yana daga cikin tsarin da suka bullo da shi na kirkiro da wani ofishi na musamman domin taimaka ma wadanda suka samu rauni ko rasa rayuka saboda matsalar ‘yan ta’adda.
Tun da farko a cikin jawabinsa babban mai ba gwamna shawara kar harkokin mutanen da suka fuskanci matsala saboda ‘yan ta’adda, Sa’ idu Danja, ya ce gwamnati ta bada tallafin kudi Naira milyan 20 domin bada tallafi ga iyalan jami’an da suka mutu da kuma wadanda suka samu rauni a wajen arangama da yan ta’adda.
Danja, ya ce iyalan jami’an rundunar sintiri 33 da aka kashe zasu samu tallafin dubu dari 5 kowane, sai iyalan sojojin da aka kashe zasu samu milyan daidai sai kuma wadanda suka samu rauni za a basu tallafin dubu dari biyu da hamsin.
