Warin Bakin Ango, Ya Sanya Amarya Taƙi Yarda Ya Sumbace Ta Ana Tsaka Da Bikin Aure
Bidiyon ya ba da labarin wata amarya da ta ki sumbatar angonta saboda tana zargin bakinsa na da wari.
Mutumin ya yi iya kokarinsa, amma matar ba ta bar shi ya dasa mata lebbansa ba.
Daga karshe ango ya fito ya bayyana cewa matar tana jin kunya kuma ba ta san yadda za ta sumbace shi a cikin jama’a ba.
Ma’auratan sun fito suna nuna farin cikin su da yadda suka zama abin magana.
Cikin murmushi suka ce a cikin wani faifan bidiyo,
Muna godiya ga ‘yan Ghana bisa ayyukan da kuka yi mana, kun sanya mu shahara sosai, don haka muna godiya a gare ku
