Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar cewa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, zai jagoranci Hawan Idi na wannan shekarar a cikin shirye-shiryen bukukuwan Sallah.
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya ya fitar a ranar Laraba, gwamnatin ta ce Hawan Idi zai fara daga filin Sallar Kofar Mata, sannan ya bi hanyoyi da aka tanada zuwa fadar Sarkin Kano.
Sanarwar ta zo ne yayin da aka kara tsaurara matakan tsaro, inda gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gargadi kan yiwuwar wasu mutane su tada rikici a yayin bukukuwan Sallah.
Gwamnatin ta jaddada cewa yayin da take kokarin kare al’adun gargajiya na Kano, kiyaye zaman lafiya da oda shi ne babban abin fifiko.
A karkashin matakan da aka tsara, Hawan Nasarawa zai gudana amma ba za a yi shi da dawaki ba, yayin da Hawan Daushe, Hawan Fanisau, da Hawan Dorayi aka dakatar da su a wannan lokaci domin tabbatar da tsaro.
An umarci hukumomin tsaro su kara lura sosai, su tabbatar da bin ka’idojin da aka shimfida kafin, yayin, da bayan bukukuwan Sallah.
Gwamnatin ta yi kira ga al’umma da su kasance masu biyayya ga doka, su yi aiki tare da jami’an tsaro, tare da kauce wa yada bayanan da ba a tabbatar da su ba, sannan ta tabbatar da cewa za a gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana.
