Wani Harin Kwantan Ɓauna Ya Hallaka Soji 3 Da Ƴan Bindiga Da Yawa

Wani Harin Kwantan Ɓauna Ya Hallaka Soji 3 Da Ƴan Bindiga Da Yawa A Zamfara

Daga Amira Salisu Batsari.

Ƴan bindiga a ranar Laraba sun ƙaddamar da harin Kwantan ɓauna ga Sojoji a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, tare da kashe Soji uku.

Mazauna yankin sun ce ƴan bindigar ɗauke da Makamai sun yi harin Kwantan ɓauna akan Motar Sojoji a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Fanda-Haki, Ƴar Katsina ta Al’ummomin Karrakai.

” An sanar da sojojin harin da akai kai a yankunan sai suka yanke shawarar zuwa wurin da aka kai harin domin su dakatar da lamarin kawai suna cikin tafiya sai sukaji yan ta’adda sun buɗe masu wuta, inji wani mazaunin yankin Mai suna Hussain Ali.

Mazaunin yankin ya bayyana cewa sojojin sun maida wuta tare kashe yan bindiga da dama, wanda ƙarfin bindigar Sojin ta sanya Ƴan Bindiga suka ruga.

Mai Magana da Yawun Sojoji a Jihar Kaftin Ibrahim Yahaya ba’a same shi domin magana a lokacin da haɗa wannan rahoton, a yayinda wayar sa ta kasance a kashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *