Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Matsalar Tsaro na Ƙasa

A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron kwamitin tsaro na kasa (NSC) a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa taron dai shi ne karo na biyu tun bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ke Abuja, wanda ya kai ga sakin ‘yan tada kayar baya da dama.

A taron da ke gudana a cikin zauren majalisar akwai sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro DSS, Yusuf Bichi; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abu, da sauran manyan hafsoshin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *