Zaɓen Osun: EFCC Tayi Dirar Mikiya A Wuraren Da Ake Kaɗa Ƙuri’a

Zaɓen Osun: EFCC Tayi Dirar Mikiya A Wuraren Da Ake Kaɗa Ƙuri’a

Wasu jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun ce suna lura da abubuwan da ke faruwa a zaben gwamnan jihar Osun da ke gudana a yau.

Kimanin jami’an hukumar shida ne suka isa makarantar firamare ta mazabar Saint Peters 1, shiyya ta daya, Iragbiji, a jihar Osun.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa, an hangi jami’an ne lokacin da ake ci gaba da kada kuri’a.

Da isar su, daya daga cikin jami’an da wakilinmu ya tuntube shi ya mika shi ga shugaban tawagar, inda shi kuma ya ce, “muna nan ne domin mu lura da kuma lura da abubuwan da ke faruwa. Har yanzu bamu kama kow ba.”

Jami’in ya ce, sun samu mata da wani zargi na daban, amm ta ki bayyana sunanta kuma ta ki yin karin bayani duk da kokarin samun karin haske daga gare ta.

Haka kuma a Ward 1 Unit 2, Popo, Iragbiji, inda Gwamna Adegboyega Oyetola ya kada kuri’a, an kuma ga jami’an EFCC, nan ma suna ta shawagi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *