APC ta musanta zargin da NNPP Kwankwasiyya ta yi mata kan batun shari’a

Jam’iyyar APC ta karyata zargin da NNPP Kwankwasiyya ta yi na cewa gwamnatin jihar Kano na yin katsalandan a harkokin shari’a don ya yi daidai da buƙatar ta, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya da ɓata suna.

A cikin wata sanarwa da kakakin APC a Kano, Auwalu Soja Gwale, ya fitar, ya ce zargin da aka rawaito cewa kakakin NNPP, Ibrahim Karaye, ya yi ba shi da wata hujja, kuma an yi shi ne da nufin bata sunan bangaren shari’a.

Jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa gwamnatin jihar Kano ta biya kuɗaɗe masu yawa akan shari’o’in da ke gudana a babbar kotun tarayya da ke Abuja don kawo wa NNPP matsaloli a zaɓe mai zuwa, tare da buƙatar a janye kalaman nan take.

Sanarwar ta kuma bai wa Karaye da NNPP wa’adin sa’o’i 72 su janye zargin, su bayar da haƙuri a bainar jama’a tare da guje wa yin irin wannan ikirari a nan gaba. Ta gargadi cewa rashin bin wannan umarni zai kai ga ɗaukar matakin shari’a kan ɓata suna.

APC ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya, mugunta kuma marar tushe a doka,” tana mai jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ba ta taɓa tsoma baki a harkokin shari’a ba.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci ɓangaren Kwankwasiyya na NNPP da ya mayar da hankali wajen warware rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar, inda ta ambaci shari’o’in da ke gudana tsakanin ɓangarorin da ke da alaƙa da Boniface Aniebonam da kuma Rabiu Musa Kwankwaso, maimakon yin waɗannan zarge-zargen marasa tushe.

A ƙarshe, APC ta jaddada aniyarta ta bin doka da oda, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da zargin, tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *