Mace Sai Da Kwalliya…

An bude sabon wurin kwalliyar zamani mai suna Glamsy.ng a Katsina.

Sabon wurin wadda fitacciyar make up artist din nan mai suna Hadiza Hassan Musa ta bude na nan a sabon titin kwado daura da daukar kaji.

Hadiza Hassan Musa ta ce ta bude wurin ne domin saukaka ma mata da yan mata nisan zango wajen tafiya domin samun hadaddar kwalliya.

A cewarta a Glamsy.ng babu abinda ba su yi na kwalliyar mace da kawata ta.

A yayin kaddamar da wajen a ranar Larabar da ta gabata, mata masu ji da kansu sun samu halartar taro tare da fatan alkhairi da kuma dauke dauke hotuna da wasu abubuwan da suka shafi nishadi a wajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *