Adoke ya nemi gwamnatin Najeriya ta ba shi hakuri kan zargin OPL 245

Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Mohammed Adoke, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta ba shi hakuri ba tare da sharadi ba, bayan shekaru na zargi da bincike kan rikicin rijiyar mai ta OPL 245 da daga bisani kotu ta wanke shi daga dukkan tuhume-tuhume.

Adoke ya bayyana hakan ne bayan gwamnatin tarayya ta sanar da warware rikicin rijiyar mai ta OPL 245, inda ya ce matakin na tabbatar da cewa rawar da ya taka wajen sasanta rikicin a shekarar 2011 ta kasance cikin gaskiya. Ya ce yarjejeniyar da aka cimma a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta yi kokarin kawo karshen takaddamar da ta dauki kusan shekaru da dama tana jan hankali.

Ya kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakin warware rikicin rijiyar mai mai dimbin arziki, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunkasa samar da mai a Najeriya. Fadar shugaban kasa ta ce yarjejeniyar na iya kara kusan ganga 150,000 na mai a kowace rana a karfin samar da man kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *