An kama lauyan Emefiele da dala miliyan biyu – EFCC a kotu

Wani jami’in bin cike na Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ya shaida wa babbar kotun FCT High Court cewa sun kama wani lauya da fiye da dala miliyan biyu, wanda ake zargin kudin na tsohon gwamnan Central Bank of Nigeria (CBN), Godwin Emefiele ne.

Shaidan, David Jaiyeoba, ya bayyana cewa an kama lauyan mai suna Collins Omeife da dala $2,045,000, kuma yayin tambayoyi ya tabbatar cewa kudin na Godwin Emefiele ne, wanda ake tuhuma da laifuffuka 20 da suka hada da almundahana, zamba da kuma karya doka a lokacin da yake shugabantar CBN. Ya ce an tura kudin gare shi ne ta hannun mataimakin Emefiele, Eric Ocheme, domin saye da gyaran kadarori a Lagos da wasu wurare.

Jami’in EFCC ya kuma fada wa kotu cewa an yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen saye da gyaran gidaje a Lekki da Ikoyi da kuma wani ginin masana’antu a Agbor, Delta State. Sai dai Emefiele ya musanta dukkan zarge-zargen, yayin da alkalin kotu Hamza Muazu ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga Maris domin ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *