Ambaliyar ruwa a shekarar 2022 a Najeriya ta yi ajalin mutane sama da 300 a jihohi da dama har zuwa watan Satumba, a cewar wani rahoto daga kungiyar Save the Children.
Babbar kungiyar agaji da ke da hedkwata a Birtaniya ta ce akalla mutane 75 ne suka mutu a jamhuriyar Nijar makwabciyar Najeriya.
Hukumar ta kiyasta cewa sama da mutane 150,000, wadanda kusan rabinsu yara ne, ambaliyar ruwa ta shafa a kasashen biyu.
Mamakon Ruwan saman da aka tafka a kudancin Nijar da arewacin Najeriya ya janyo mummunar barna ga rayuwa da gidaje da amfanin gona da kuma dabbobi.
Ambaliyar ruwa ta lalata al’ummomi da dama a kan iyakar Nijar da Najeriya, tare da lalata gidaje kusan 14,500.
Yankunan da abin ya shafa a Nijar sun hada da Maradi, Zinder, Tillaberi da Tahoua; Jihohin Adamawa, Borno, Jigawa, Kogi, Yobe, ne suka gamu da iftila’in a Najeriya.
Rahoton ya ce a Yobe, mutane miliyan 1.6 wato kusan kashi 40 na al’ummar kasar ne suka shiga cikin gararanba.
