Yan sanda a Katsina sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi, da suke zargi da safarar harsasai ga yan ta’adda da ke cikin daji a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ASP Sadiq Abubakar ne ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a hedikwatar yan sandan da ke Katsina.
Ya ce mai laifin da aka kama shi ya ce ya je garin wukari a jihar Taraba inda suka samu wani mai suna Salisu a garin kuma ya basu wadannan harsasai domin su kai ma yan ta’adda n cikin daje.
Sai dai mai laifin ya ce saboda tsoron hukunci da zai fuskanta a wajen wanda ya basu sakon shi yasa ya karba duk da kuwa ya san cewa dan ta’adda ne.
Ya ce shi da farko bai san sakon ko na menene ba, sai bayan da jami’an tsaro suka kama shi suka kwance gaban shi san nan ya ga abinda sakon ya kunsa cewa harsasai ne na bindiga ya karbo.
Wannan mutum dai yana da mata biyu da yara.
