Tsoho Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri, ya ce duk girman mutum a Najeriya zai bar jam’iyyar PDP inda ya gan ta.
Wannan na zuwa ne a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Katsina game da maganar hukuncin kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta yanke ga yan majalisun su na tarayya da suke zargin APC ce ke masu zagon kasa.
Sanata Tsauri ya ce tsohon shugaban Najeriya, janaral Olushegu Obasanjo yana gidan yari aka fiddo shi amma ya ci zaben shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, ya ce kuma sai da ya ya kwashe kimanin shekaru 8 yana mulki.
Ya ce amma duk da wannan shekarun da ya kwashe yana mulkin ya nemi ya yi tazarce aka hana shi, wanda hakan ya ja ya yi abinda duk duniya ba a taba yi ba, na yaga katin jam’iyyar da ita ya shekara 8 yana mulki.
Sanatan ya ce ita PDP, ba jam’iyyar son rai ba ce son haka ba a barin mutum ya yi abinda ya ga dama a cikinta.
A don haka ya ce duk abin mutum zai gaji ya barta a inda ta ke.
