Wazirin Katsina na 5 Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya shawarci gwamnatin tarayya da Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC na Najeriya da su rinka sara ana dubar bakin gatari.
Farfesan ya yi wannan kira ne a yayin wata zantawa da ya yi da Jakadiya a gidansa kan batun karin albashin watanni shida da gwamnatin shugaba Tinubu ta ce zata yi wa ma’aikatanta.
Ya ce, ya kamata gwamnati da Kungiyoyin su san cewa ba ma’aikatan gwamnati kadai ba ne yan Najeriya a kwai mutum milyan dari 224 kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana.
Lugga, ya ce halin matsi na tsadar rayuwa da ake ciki a kasar ya shafi wadannan mutane milyan dari 224 dukkansu ba wai ma’aikata ne kadai ke cikin wahala ba.
Ya ce hasali ma ma’aikatan gwamnatin tarayya su dubu dari 720 ne.
A don haka Farfesa Lugga ya ce wannan tsari na kara wa ma’aikatan gwamnatin su kadai albashi shima na tsawon watanni 6 ba zai maganin matsalar da ake ciki ba.
Ya ce ya kamata gwamnati ta tuntubi duk wadanda suka dace domin a yi maganin matsalar tsaro da hauhawar farashi da ma sauran matsaloli da yan kasar suke ciki.
Daga karshe ya yi kira ga kungiyar ma’aikata da cewa duk wata tattaunawa da za ai kamata ya yi su yi a madadin yan Najeriya gaba daya ba ma’aikatan Gwamnati kadai ba.
Gwamnatin Najeriya dai ta bakin shugabanta, Bola Ahmed Tinubu ta ayyana cewa zata yi wa ma’aikatanta karin kudi Naira 2,5000 har tsawon wata shida kafin daga bisani ta kara yawan kudin zuwa 3,5000 kamar yadda rahotonni suna ruwaito.
