Ci Bayan Da Najeriya Ke Samu Ba Shugabanni Kadai Ke Da Laifi Ba – Maiwada Dammallam

Darakta Janar na kafafen yada labarai ga gwamnan jihar katsina Dr. Dikko Umar Raɗɗa, Maiwada Dammallam ya bayyana cewa Najeriya na samun ci gaban mai gina rijiya idan aka kwatanta yadda kasar ta ke a shekarun baya.

Dammallam ya ce, tun daga juyin mulki na farko da ya tuntsurar da gwamnatin farar hula ta su Sardauna to idan ma mutum ya ce daga duk mulkin da aka yi kasar ta samu ja baya to bai yi kuskure ba.

Ya ce ya san da yawa daga cikin mutanen da suka ritso wancan mulkin na baya in da za a ce masu an basu dama su zabi a koma baya ko a dasa daga inda ake yanzu a kasar to zasu zabi a koma baya din.

Sai dai Dammallam ya ce wannan matsala ta rashin samun ci gaba a Najeriya ba laifin shugabanni ba ne kadai har da laifin yan kasar, ya ce saboda ba a samun gurbatattun shugabanni sai an samu bara gurbin yan kasa.

Ya ce mafiyawan masu zagin gwamnati wadanda gwamnatin bata yi wa dadi ba ne amma da zaran mutum ya samu shiga to babu ruwanshi da ko al’umma su samu ko kar su samu.

Ya ce mutane in dai ba su aka yi ma wa ba to duk kokarin gwamnati ba zasu gani ba sai dai su ga gazawarta.

Ya ce ya kamata mutane su gyara halayensu su yi abinda ya dace wajen gyaruwar kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *