Babban Bankin Najeriya CBN ya umurci bankunan kasuwanci a kasar da su dinga yin aiki a ranakun Asabar har zuwa ranar 31 ga watan Junairu, 2023, domin baiwa kwastomomi damar dawo da takardun Naira da suke da su.
Babban bankin na CBN ya bayyana shirin sake fasalin takardun kudi na N200, N500, da N1,000, tare da fitar da sabbin takardun kafin ranar 15 ga watan Disamba, 2022.
Da yake jawabi a wajen bikin baje kolin na CBN a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ranar Alhamis, Daraktan CBN, Sashen Sadarwa, Osita Nwasinobi, ya ce sabbin takardun da ake da su za su ci gaba da kasancewa a kan doka har zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2023, lokacin da takardun da ake da su za su daina aiki.
Taken Baje kolin na CBN,shine “Samar da daidaiton harkokin kudi da bunkasar tattalin arziki.”
