Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal a ranar Lahadi ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta na jihar Ogun.
Sun hadu ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) Penthouse na tsohon shugaban.
Sanarwar da mai magana da yawunsa Kehinde Akinyemi ya fitar ta ce Tambuwal ya isa ne da misalin karfe 1:30 na rana tare da wasu manyan mukarrabansa.
Gwamnan da mai masaukinsa sun kammala taron da misalin karfe 2:40 na rana, inda ake saran sun tattauna batutuwan da suka shafi kasa.
Obasanjo ya ci abincin rana tare da bakon nasa wanda daga baya ya yi sallah a masallacin da ke cikin OOPL kafin ya bar harabar.
