Daraktan NPC na jihar, Balarabe Kabir, ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da masu horaswa da aka gudanar a Kano.
Ya ce an shirya taron ne tare da hadin gwiwar ALGON da NIMC, tare da tallafin UNICEF da gwamnatin Netherlands.
Kabir ya kara da cewa, baya ga wannan adadi, an kuma yi rajistar yara kusan 27,000 ‘yan kasa da shekara biyar, da sama da 40,000 da suka haura shekaru biyar da ba a taba rajista ba a baya.
Ya ce an shirya taron ne domin kara inganta kwarewar masu rajista a kan amfani da tsarin rajistar bayanai na zamani a kananan hukumomi 44 na jihar.
Sai dai ya bayyana wasu kalubale da suka hada da matsalar tsarin na’ura, jinkirin tabbatar da lambar NIN da kuma karancin tallafi ga ma’aikatan da ke aiki a yankunan karkara.
Kabir ya jaddada cewa rajistar haihuwa hakki ne na kowane yaro, kuma tana da matukar muhimmanci wajen tsaro, tsare-tsare da samun ayyukan jin kai.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun ce horaswar ta kara musu ilimi da dabarun zamani da za su taimaka wajen inganta rajistar haihuwa musamman a yankunan karkara.
