Mafi Akasarin Matan Jahar Katsina Dikko Raɗɗa Za Su Zaɓa A 2023 – Mustapha Raɗɗa

Mai sharhi akan al’amurran siyasa da ke Katsina a Arewacin Najeriya, Mustapha Raɗɗa, ya ce Dikko Radda shi ne zai lashe zaɓen shekarar 2023 a jahar Katsina.

Ya bayyana yiwuwar samun nasarar Dikkon ne a yayi wata fira da ya yi da kafafen sadarwa na zamani da suka haɗa Jakadiya da Katsina Post da Qlic Media da Mobile Media Crew, a ranar talatar nan da ta gaba a ofishin Qlic Media da ke da mazauni a Katsina.

Raɗɗa ya ce duba da yadda mutane suka raja’a da nuna sha’awarsu ga Dikko Raɗɗa Musamman ma matan jahar ta Katsina waɗanda mafi yawancinsu Dikko su ke da sha’awar su zaɓa a matsayin Gwamna

A don haka ya ce shi yana gani cewa APC ita ce ke da nasara a zaɓen da ke tafe na 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *