Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin rashin da’a a aiki, saba ka’idar ofis da kuma cin amana.

Rahotanni sun nuna cewa akalla ‘yan majalisa 38 ne suka sanya hannu kan takardar neman tsige shi, wadda aka gabatar a zaman majalisar bisa tanadin sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

A cikin takardar, ‘yan majalisar sun zargi Gwarzo da karɓar kuɗaɗe daga ƙananan hukumomi 44 na jihar tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024, inda ake zargin yana karɓar kimanin Naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma a kowane wata.

Haka kuma, takardar ta zarge shi da karɓar wasu kuɗaɗe da suka kai Naira miliyan 726 tsakanin Fabrairu zuwa Yulin 2024 da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman ga ƙananan hukumomin.

Bugu da ƙari, majalisar ta ce mataimakin gwamnan ya taimaka wajen fitar da Naira miliyan 440 daga kuɗaɗen ƙananan hukumomi zuwa kamfanin Novomed Pharmaceuticals Limited, lamarin da ta ce ya saɓa da dokokin saye da kashe kuɗaɗen gwamnati.

Majalisar ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge sun kai matakin babban laifi a aiki, don haka ta fara matakan tsige mataimakin gwamnan bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *