NDLEA ta kama kwayoyi da aka boye a cikin jaket na sanyi da man shafawa a filin jirgin sama na Legas

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun dakile yunkurin wasu kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi na fitar da haramtattun kwayoyi da aka boye a cikin bangon kwali, jaket na sanyi da kwalaben man shafawa a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, da kuma wani kamfanin aika kaya da ke birnin.

Hukumar ta ce an kama kaya biyu da ake shirin aikawa kasar Italiya a filin jirgin saman Legas, lamarin da ya kai ga cafke wasu mutane da ake zargi suna da hannu a lamarin.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an cafke daya daga cikin wadanda ake zargin, Friday Ehianuka mai shekaru 37, a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026, yayin da yake kokarin shiga jirgin Ethiopian Airlines zuwa Rome, kasar Italiya.

Sanarwar ta ce “An shirya jigilar wasu daga cikin kayan biyu da ake kai wa Italiya ne ta filin jirgin saman Legas, inda aka gaggauta cafke mutane biyu da ake alakanta su da kayan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *