Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Shehu Umar Nadada, ta mika chakin kuɗaɗe da darajar su ta kai kimanin nera miliyan 54 da dubu 532 ga iyalan ‘yan sandan da suka rasa rayukan su a yayin gudanar da ayyukan su na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar nan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Nadada ne ya mika chakin kudaden ga waɗanda suka amfanan a ranar Juma’ar nan a hedikwatar rundunar da ke Katsina a madadin Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Alkali Baba Usman.
Tallafin kudaden dai yana fitowa ne karkashin wani shirin inshorar rai na shugaban ‘yan sandan, wato ” IGP Group Life Assurance Scheme” a turance.
A yayin miƙa chakin kuɗaɗen CP Umar Nadada ya gode wa Sufeta Janar din bisa yadda yake nuna damuwar sa wajen tabbatar da jin daɗin jami’an rundunar.
Ya kuma bayar da tabbacin rundunar ‘yan sandan da ma sauran hukumomin tsaro na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar musamman ma wadanda ke yankunan da ke fama da matsalar ta’addanci da satar jama’a da dabbobi.

