Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Tsohon Gwamnan jihar Kano wanda a yanzu shine sanata mai wakiltar kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau ya koma jam’iyyar PDP.
Shekarau ya koma jam’iyyar ne a Majalisar Dattawa a lokacin zaman Majalisar a ranar Laraba.
Kafin ya koma jam’iyyar, memba ne a jam’iyya Mai Alamar kayan Marmari wato NNPP.
Tunda farko dai yabar jam’iyyar APC inda ya koma Jam’iyyar NNPP.
