Shugaba Buhari Yayi Zazzafan Kalamai Kan Kisa A Yankin Inyamurai, Ya Buƙaci Malamai Su Tashi Tsaye

Shugaba Buhari Yayi Zazzafan Kalamai Kan Kisa A Yankin Inyamurai, Ya Buƙaci Malamai Su Tashi Tsaye

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace dole Mutane da Malaman Addini su nuna ɓacin rai da Allah-wadai, tare da ƙara azama kan Yaƙar kashe-kashen dake faruwa a yankin Kudu maso Gabashin Ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a cikin wata takarda da mai taimaka masa na Musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

Shugaban Ƙasa ya alwashin cewa, Gwamnati na gudanar ɗaukar matakai gami da bincike don gurfanar da masu aikata laifin a gaban kotu.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa an hallaka wasu ƴan kasar Nijar shida da ƴan sanda a bakin aiki.

“Ya kamata al’umma da malaman addini su ƙara yin magana kan kashe-kashen, dole mu tashi tsaye mu kare al’adunmu da addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *