Sojin Sama Sun Hallaka Ƴan Bindiga Masu Yawa a Dajin Zamfara

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Jiragen yaƙi guda biyu na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya sun hallaka Ƴan bindiga masu yawa da ake kyautata zaton cewa mambobin Kwamandan yan ta’adda ne Bello Turji a dajin Zamfara.

A cewar wata Majiya, an hallaka ƴan bindigar ne a lokacin wani samamen harin da Rundunar sojin sama ta Operation Foret Sanity ta kai a jihar Zamfara.

Harin na ban mamaki da jami’an sojin suka kai ya ƙunshi jiragen yaki biyu masu saukar ungulu, biyo bayan bayanan sirri da aka samu.

A cewar wata majiyar sirri daga Hukumar tsaro, Jirgin Sojin Saman ya saki ruwan bama-bamai a yankin Fakai, inda aka tabbatar da cewa, wurin Kwamandan Ƴan bindiga ne, Bello Turji.

” A wannan lokacin ba zamu iya bada iyakar yawan waɗanda aka hallaka” Inji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *