Tinubu Yace Dole APC, Dashi Suyi Wani Yunƙuri Kafin Zaɓen 2023

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bukaci ‘yan jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Gabas da su kara kaimi kafin zaben 2023.

Ya bayyana haka ne a Gombe ranar Asabar a wajen liyafar daurin auren Misbahu Yahaya dan Gwamna Inuwa Yahaya.

Tsohon Gwamnan na Legas ya tunatar da magoya bayan jam’iyyar APC cewa abokin takararsa Kashim Shettima ya fito daga yankin.

Tinubu ya godewa ‘yan jam’iyyar da magoya bayansa kan abin da suke yi masa.

A nasa bangaren Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana yankin Arewa maso Gabas a matsayin shiyya ta biyu ga Tinubu bayan Kudu maso Yamma.

Shettima ya ce nan ba da dadewa ba za a fara gangamin siyasa, inda ya kara da cewa, Arewa-maso-Gabas yanki ne na APC don haka zasu yi duk mai yiwuwa domin nasarar jamiyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *