Rundunar Ƴansandan Jihar Borno ta tabbatar da rasuwar mutane 23, yayin da wasu 108 suka jikkata a garin Maiduguri sakamakon tashin bama-bamai da suka faru a jiya Litinin.
Rundunar ta bayyana cewa ana zargin wasu masu kai harin kunar bakin wake ne su ka tada bama-baman da misalin ƙarfe 7:24 na yamma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Nahum Daso ne ya bayyana a cikin wata sanarwa, inda ya ce cewa binciken farko ya nuna cewa maharan sun yi amfani da bama-bamai ƙirar gida (IEDs).
Daso ya ce an kai hare-haren ne a babbar kasuwar cikin garin Maiduguri, wadda aka fi sani da Monday Market, sai ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da kuma yankin gadar sama na ofishin Post Office a cikin garin.
A cewarsa, an tura haɗaɗɗiyar tawagar jami’an rundunar ƴansanda na musamman da sojoji, da sauran jami’an tsaro zuwa wuraren da lamarin ya faru cikin gaggawa.
sakamakon tashin bama-bamai da suka faru a jiya Litinin.