Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua. Daga shiyyar Katsina, jihar Katsina, ya ankarar da gwamnatin tarayya cewa yanzu ne lokacin da ya kamata a samar da Yan Sandan jihohi.
Sanatan ya ce , ba zai yuwu a zuba ido ana rasa rayuka da dukiyoyin al’umma ba sakamakon aikace aikacen ya ta’adda.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sanatan, ya ce, samar da yan sandan jahohi a yanzu abu ne da zai taiamaka kwarai wajen kawar da matsalar tsaro, musamman yadda za a rika samun hanzarin kai dauki idan an samu labarin kai hari ko ma shiri a kan hakan.
Sanata ya kuma shawarci, Gwamnonin jahohi da kananan hukumomi da su kara matsa kaimi wajen tallafa wa jami’an sa kai domin yin aiki tare da yansanda don kawo karshen matsar tsaro.
