Zan Kori Duk Wanda Ya Zanja Sunan Wani Daga Cikin Ma’aikatan S-POWER Da Za A Dauka Aiki – Dikko Raɗɗa

Gwamnan Jihar Katsina Dr, Dikko Umar Raɗɗa ya ja kunnen masu kula da alhakin tabbatar da shirinsa na daukar malaman makaranta sama da dubu 7 da yawa daga cikinsu wadan da ke cikin tsarin nan na S-POWER ne a jihar.

Gwamnan ya yi wannan jan kunnen ne a yayin ganawa da jagororin shirin daukar malaman a fadar Gwamnatin jihar a ranar Talatar da ta gabata.

“Wallahi duk wanda ya cire sunan wani ya sanya sunan wani to shi ma yana iya rasa aikinshi kan wannan abin da ya yi, ba sani ba sabo.” Inji shi.

Radda ya ci gaba da cewa. “Ba zamu bata lokacinmu da kudin gwamnati ba a yi wannan aikin wani yana zaune ofishinshi ya zanja mana sunan wani.” ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *