Zamu Dago Tattalin Arziki Har Ya Zama Ba Sauran Mai Bara A Najeriya – Shettima

Zamu dawo da tattalin arziki yadda babu dan Najeriya da zai yi bara – Inji mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin da ke mulki yanzu a karkashin tutar Jam’iyyar APC zata yi duk mai yiwuwa domin dawo da tattalin arzikin kasar.

Kashim Shettima na wannan bayanin ne a daidai lokacin da ake shagulgulan cikar kasar ta Najeriya shekaru 56 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

BBC ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar ya ce idan suka dago martabar tattalin arzikin sai kasar ta koma babu wani danta da ke bara saboda wadata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *