Ambaliyar ruwan da ta afku a baya-bayan nan ta kashe akalla mutane 50 a cikin al’ummomi 11 da ke jihar Adamawa tare da jikkata wasu 71.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa ADSEMA, Malam Suleiman Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Yola lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN.

Ya daura laifin ambaliya a kan sako ruwa daga Lagdo Dam da ke makwabtaka da kasar Kamaru.

Mohammed ya kuma ce ambaliyar ta lalata gonaki 172,000 da kayan abinci na miliyoyin naira.

Wasu daga cikin kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Numan, Shelleng, Yola ta kudu , Yola ta arewa, Demsa, Mayo Belwa da Michika.

Ya kara da cewa hukumar ta samar da kayan sawa, kayan abinci, magunguna, gidajen sauro, barguna ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *