Wani Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane Biyar A Jihar Anambra

Wani Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane Biyar A Jihar Anambra

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Wata yarinya da Matasa hudu sun rasa ransu sakamakon wani hatsari akayi a daren ranar Lahadi, wanda ya rutsa da wata motar jeep da Babbar Mota akan babbar hanyar Enugu -Agidi akan Babbar hanyar Awka Enugu .

Shugaban Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa reshen Jihar Anambra Mr Adeoye Irelewuya ya tabbatar da faruwar lamarin a garin Awka ga Kamfanin Dillancin labarai a ranar Litinin dake Awka.

Irelewuya ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a dalilin mugun gudun da kuma kasa shawo kan Motar.

“Hatsarin ya hada da wani direban da ba’asan ko wanene ba wanda yake cikin wata bakar Motar ƙirar Lexus mai lamba KJA182HS da kuma wani direban Babbar Mota ‘Ja’ wadda bata da lamba.

“Acewar wani wanda ya shaida lamarin ya bada rahoton cewa direban babbar motar ya rasa damar shawo kan motar sakamakon mugun gudun daya keyi inda ya afkawa karamar motar kirar Lexus SUV.

“Kimanin mutane biyar hatsarin ya rutsa dasu wanda ya ƙunshi, Maza ukku da Mace ɗaya da kuma yarinya, dukkaninsu sun rasa ransu.

” Wata tawaga ta Jami’an Hukumar ƙare hadurra ta kasa na yankin suka ɗauki mutanen zuwa a asibitin Koyarwa na Chukwuemaka Odumegwu Ojukwu, na Amaku dake Awka, yayin da likitan dake aiki lokacin ya tabbatar masu da mutuwarsu, inda aka kai gawarwakin a dakin ajiye gawa na asibitin,” Inji shi.

A lokacin da yake ta’aziyya ga iyalan mamatan shugaban hukumar, yayi gargadi direbobi musamman direbobin manyan motoci dasu daina mugun gudun da suke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *