Yanzu-Yanzu:Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Ƙarin Kuɗin Kiran Waya Da Na Saƙon Karta Kwana

 

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Pantami ne ya sanar da dakatarwar a yau Litinin yayin taron kaddamar da kwamitin shugaban kasa haraji kan hanyoyin sadarwa don bunƙasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja.

Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa.

Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin kasafin kudi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da shirin fitar da kudaden da ta ke bukata a kan harkokin sadarwa da abubuwan sha a shekarar 2023.

Sai dai Pantami ya ci gaba da cewa ba ya goyon bayan aiwatar da wannan harajin da zai kara tsadar harkokin sadarwa ga ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *